Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwar Gobarar Daji Ta Tashi A Jihar California


Hughes Fire, Castaic Lake
Hughes Fire, Castaic Lake

Gobarar dajin ta fara ne da safiyar ranar Laraba, kuma ta kone daruruwan kadadar bishiyoyi, sannan hayaki da burbushin toka sun turnuke yankin Castaic Lake.

Hukumomi a California sun ba da sanarwa ga al’ummomin da ke daura da Castaic Lake da su fice daga yankin, bayan da wata sabuwar gobarar daji ta tashi a tsaunukan arewacin Los Angeles.

Kudancin California yana fama da tashin gobara saboda busasshiyar Iska da rashin samun ruwan sama.

Sannan hukumomi sun yi kira ga al'ummar yankin da su kaurace wa kusa da yankin saboda shakar gurbataccen hayaki.

A halin da ake ciki, akwai gargadi game da yiwuwar tashin wata mummunar gobarar a kudancin California.

Dr. Talatu Bako 'yar Najeriya da ke zaune a Los Angeles, California ta shaida wa Muryar Amurka cewa gobarar ta yankin Castaic Lake ta yi barna sosai, kuma hukumomin kashe gobara su na ta fafatawa wajen shawo kanta.

Saurari tattaunawa da Helen Bako cikin sauti:

INTERVIEW WITH HELEN BAKO CALIFORNIA RESIDENT.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG