Wata tawagar babban jami’in kasar Amurka ta isa kasar Kenya domin tantance illar fari da ake fama da shi a yankin da kuma tattaunawa kan matakan shawo kan lamarin. Tawagar dake karkashin jagorancin uwargidan mataimakin shugaban kasa Jill Biden ta isa Kasar Kenya ne yau Litinin da safe, daga nan Mrs. Biden zata tafi sansanin ‘yan gudun hijira dake Dadaab, inda dubun dubatan Somaliyawa da yunwa ta tilastawa kauracewa matsugunansu suka yada zango a cikin makonnin nan. Fadar shugaban kasa tace, ziyarar ta Mrs. Biden zata jadada kudurin Amurka na taimakawa mutanen kuryar arewa maso gabashin Afrika da farin ya shafa. Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane miliyan daya ne daga yankin ke matukar bukatar agajin abinci. Kasar Kenya bata fuskantar yunwar da ta bazu a kudancin Samaliya, sai dai Majalisar Dinkin Duniya tace wadansu sassan kasar suna fuskantar barazanar karancin abinci. Fadar shugaban kasa ta White House tace uwargidan mataimakin shugaban kasa Jill Biden zata gana da shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki da kuma Firai MinistaRaila Odinga domin tattaunaw akan hanyar shawo kan matsalar.