Cibiyar samarda abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta WFP tace tana nan tana kokarin hanzarta kai agajin kayan abinci ga mutane sama da milyan 12 dake fama da matsananciyar yunwa a wasu kasashen Afrika. A ranar Talatar nan ne cibiyar WFP take bada sanarwar cewa zata soma jigilar, kuma zata soma ne da Mombasa ta Kenya inda zata kai wani nau’in wani biskit dake tattare da abubuwan gina jiki a cikinsa, inda kuma zata kai isasshen da za’a iya ciyarda mutane milyan 1 da dubu 600 kowace rana. Haka kuma WFP tace tana shirin aika irin wannan kayan abinci mai yawa zuwa Somalia a cikin wattani biyu nan gaba, musaman don agazawa yara kanana ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa, wandanda ke fama da rashin abinci mai gina jiki.
MDD ta ce zata kara kaimi wajen kai kayan abinci ga kasashen Afrika dake fama da yunwa.