Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu ‘yan gudun hijiran Somaliya na kwarara zuwa kasar Kenya duk ko da kokarin da ake na rage matsalolin da fari da yinwa ke haddasawa a kudancin Somaliya.
Ofishin Harkokin Ayyukan Jinkai na Malalisar Dinkin Duniya y ace a mako na farko a watan nan na Agusta, kimanin Somaliyawa 1,500 ne ke isa sansanin ‘yan gudun hijira na Dadaab da ke arewacin Kenya.
Yawan ‘yan gudun hijiran ya karu ne tun daga watan Yuli.
Da alamar dai an kara himma a kokarin da kasa da kasa ke yin a taimakawa cikin ‘yan kwanakin nan, a daidai kuma lokacin da mayakan sa kai na al-Shabab su ka janye dakarunsu daga Mogadishu babban birnin kasar.
Da Humar Samar da Abinci da Humar kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya sun yi jigilar kayakin agaji zuwa birnin Mogadishu ta jirgin sama kuma suna shirin kara jigilar.
Ofishin Kula Da Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya din ya yi gargadi yau Laraba cewab har yanzu fa ana bukatar gudunmowar dala miliyan dubu 1 da miliyan 4 don yakar fari a yankin, wanda ya jefa muatane wajen miliyan 12 cikin bukatar tallafin gaggawa.