Shaidu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Mogadishu babban birnin kasar Samaliya sun ce a kalla mutane bakwai suka mutu yayin wani wasoso da aka yi lokacin da ake rabawa wadanda yunwa ta tagayara abinci. Mutanen da ke wurin sun ce an fara tashin hankali ne lokacinda wani mutum da ya yi shigar burtu ya fara satar abinci a sansanin Badgbado, sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma dake babban birnin kasar. Shaidu sun ce dakarun dake goyon bayan gwamnati wadanda ke gadin abincin sun bude wuta kan masu warwason abincin, abinda ya haddasa musayar wuta. Wadansu rahotannin na nuni da cewa an harbi wadansu mutane dake jira su karbi abinci. Fadan ya barke ne a wata cibiyar da cibiyar samar da abinci ta duniya take raba abinci. Majalisar Dinkin Duniya tayi kiyasin cewa, akalla Samaliyawa dubu goma ne suka kaurace zuwa Mogadishu kwanan nan domin neman abinci da ruwan sha. Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yunwa a yankuna biyar na kudancin Somaliya. Yayinda cibiyar ta duniya ta kuma yi kiyasin cewa, yunwa zata bazu zuwa wadansu sassan, za a kuma ci gaba da fama da ita har zuwa watan Disamba.
Shaidu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Mogadishu babban birnin kasar Samaliya sun ce a kalla mutane bakwai suka mutu yayin wani wasoso da aka yi lokacin da ake rabawa wadanda yunwa ta tagayara abinci.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024