Hakan yasa jama’a ke ta tururuwa domin ganewa idanunsu wannan abin al’ajabin. Wasu daga cikin mutanen dake wannan yanki sunce an wayi gari da wannan ikon Allah, mutane sukayi ta hawa suna jijjiga amma babu alamar ko zai lotsa kasa, har takai an hau babur da doki an wuce takai amma ciyawar na anan daram dam.
Tuni dai mahukunta suka gargadi jama’a musamman masu hawa kan ciyawar da su guji yin hakan domin komai na iya faruwa, kamar yadda kwamishinan Muhalli na jihar Ogun ke cewa a ziyararsa bakin wannan kogi.
Yanzu dai kafin masana kimiyyar tsirrai ko kuma ruwa su gama tantance abinda ya faru da wannan kogi, jama’a zasu ci gaba da tururuwa domin baiwa idanuwansu abinci.
Saurari rahotan da Babangida Jibrin ya hada mana daga Lagos.