Duk da yake gwamnatin jihar tana da sha'awar kyautata baban birnin jihar tare da fadada sha'anin kasuwanci bayan da ta killace makarantun domin sha'anin tsaro, wasu iyayen yara na ganin matakin a zaman babban barazana ga tsaro da tarbiyar 'ya'yansu mata dake makarantun.
Iyayen yara da jama'ar Rujin Sambo sun fito yin zanga zangar kin amincewa da matakin da gwamnatin jihar ta dauka musamman gina shaguna a jikin katangar makarantar 'yan mata ta jeka ka dawo dake anguwar.
Wani Shehu Garba yace suna korafi ne saboda gina shaguna a katangar Makarantar Muhammad Zako ta 'yan mata ka iya zama kariya ga yarinyar da take son yin lalata. Yace tana iya shiga shago da sunan sayen wani abu amma kuma ta kulla wani abu da wani wanda ko gwamnati ta so ta hana ba zata iya ba.
Dr. Muhammad Jabbi Kilgore kwamishanan ilimi na matakin farko na jihar yace ma'akatarsa na sane da matsalar. Yace suna nan suna tattara bayanai akan lamarin a duk fadin jihar, kana su ba gwamnati shawarar yadda za'a shawo kan matsalar.
Ga karin bayani.