Shugaban Kwamitin Sanata Abdullahi Adamu ya ce lallai haka tana cimma ruwa saboda nasarorin da suke samu wajen sulhunta 'ya'yan jamiyyar a jihohin da suka ziyarta ya zuwa yanzu.
Sai dai wasu na ganin cewa da sauran rina a kaba.
Jam'iyyar APC ta yi ta ninkaya a rikice-rikice wadanda suka jefa makomarta cikin rashin tabbas, bayan da jam'iyyar ta sanar da watan Febrairu na wannan shekara a matsayin watan da za ta gudanar da taron ta na kasa.
Wani abu da ya dauki hankali shi ne, jam'iyyar ta kafa kwamitin sulhu tun watnani 3 da suke wuce, wanda zai yi kokarin dawo da 'ya'yanta da suke neman ficewa saboda wasu korafe-korafe da suka biyo bayan zabukan shugabanin Jam'iyyar daga gundumomi zuwa Jihohi kafin taron kasa da za su yi.
Akan haka Shugaban Kwamitin Sulhu, Sanata Abdullahi Adamu ya ce kwamitin sa yana aiki tukuru wajen hada kan 'ya'yan ta.
Sai dai duk da kokarin ka kwamitin sulhu ya ce yana yi kwararru a fanin zamantakewan dan adam irin su Dr. Farouk Bibi Farouk suna ganin da sauran rina a kaba.
Abin jira a gani shi ne yadda wannan kwamiti zai kammala aikinsa a cikin lokaci saboda jam'iyyar ta samu hadin kan 'ya'yanta wuri guda a lokacin taron kasa da za ta yi domin fitar musu da shugabanni.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: