Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kamfanoni Da Cibiyoyi A Kano Sun Gudanar Da Taron Fadakarwa Kan Shaye-shayen Kwayoyi Da Kallon Fina-finan Batsa

Taron fadakar da yaran makaranta akan shaye-shaye da kallace-kallacen batsa akan intanet da shafukan sada zumunta - Jihar Kano
Taron fadakar da yaran makaranta akan shaye-shaye da kallace-kallacen batsa akan intanet da shafukan sada zumunta - Jihar Kano

A wani mataki na dakile dabi’ar shaye-shaye da kallace-kallacen hotuna da fina-finan batsa a kafofin sadarwa na intanat na zamani tsakanin yara da matasa, wasu kamfanoni da cibiyoyi masu zaman kansu a jihar Kano suka shirya taron lacca domin fadakarwa.

Taron an yi shi ne da nufin fadakarwa da wayar da kan yara da ‘yan mata game da hanyoyin kiyaye shiga cikin wadannan munanan dabi’u a shafukan sada zumunta.

Haka kuma an gudanar da taron ne domin yara dalibai da ke kanana da manyan makarantun sakandare da aka zabo daga kananan hukumomi 44 na fadin jihar Kano.

Taron fadakar da yaran makaranta akan shaye-shaye da kallace-kallacen batsa akan intanet da shafukan sada zumunta - Jihar Kano
Taron fadakar da yaran makaranta akan shaye-shaye da kallace-kallacen batsa akan intanet da shafukan sada zumunta - Jihar Kano

Fatima Sa'adina Dantata, wadda ta jagoranci shiryawa da gudanar da taron ta ce abin da suke son cimmawa a karshen taron shi ne magance wadannan matsaloli, duba da yadda alkaluman shaye-shaye da fyade a kullum suke karuwa, kuma tunatarwa da wayar da kan yara, da ilimantar da su yadda zasu kare kansu daga fadawa cikin irin wannan dabi'a suna da muhimmanci.

Engr. Mohammed Yahaya Gorki, daya daga cikin malamai da masana a fannoni dabam-dabam da suka gabatar da makala, ya ce sakon laccar shi ne mutane su san hadarin da ke tattare da fina-finan batsa, saboda akwai mutane da yawa suna kallace-kallacen irin wadannan abubuwa amma suna so su daina sun kasa, saboda kwakwalwar ta riga ta saba. Baya ga fina-finan batsa, kallace-kallacen hotunan mata a intanet da sauran wurare yana batawa mutum tunani.

"Kamar shaye-shayen kayan maye, idan mutum yana yi akan gane, amma wadanda suka saba da kallace-kallacen hotuna ko fina-finan batsa ba a iya ganewa da sauri. Wannan shi ne babban hadarin da ke tattare da kallon ayyukan batsa,” a cewar Engr. Yahaya.

Taron fadakar da yaran makaranta akan shaye-shaye da kallace-kallacen batsa akan intanet da shafukan sada zumunta - Jihar Kano
Taron fadakar da yaran makaranta akan shaye-shaye da kallace-kallacen batsa akan intanet da shafukan sada zumunta - Jihar Kano

Dr. Mohammed Auwal Haruna, na sashen koyar da aikin jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana tasirin taro irin wannan don isar da sako ga Jama’a.

”Irin wadannan taruka sukan bada damar a yi tambayoyi da kuma bada amsoshi ga mahalarta taron kuma hakan kan sanya abin da mutum ya ji, aka yi masa bayani dalla-dalla ya rike a kwakwalwar sa, har ma ya iya kai sako ga wanda bai halarci taron ba”

Cimma manufar rigakafi wadda masu salon magana ke cewa ya fi magani, ita ce hikimar zabo yara masu karanci shekaru kuma aka hallara su a zauren taron domin kubutar da su daga fada wa yanayin shaye-shaye da kallace-kallacen al’amuran batsa ta kowacce fuska, a cewar masu shirya gangamin laccar.

Dalibai maza da mata ‘yan kasa da shekaru 15 kimanin dubu guda daga makarantun gwamnati da masu zaman kansu ne suka halarci taron.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Wasu Kamfanoni Da Cibiyoyi A Kano Sun Gudanar Da Taron Fadakarwa Kan Shaye-shayen Kwayoyi Da Kallon Fina-finan Batsa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG