Hare-haren dai da ‘yan fashin dajin suka kai a karamar hukumar Mariga yayi sanadiyyar jikkata wasu mutanen da dama da kuma yin garkuwa da wasu da dama.
Sannan suka fasa shagunan mutane da kuma kona gidajen jama’a a garuruwan Gulbin Boka da Ragada da kuma garin kasuwar Garba kamar yadda wani tsohon dan majalisar dokokin Jihar Nejan dan asalin yankin Hon. Usman Musa ya shaida mana.
To amma kokarin samun karin haske daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Nejan akan wannan sabon hari yaci tura. Amma Gwamnatin jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta ce tana kokarin shawo kan wannan matsala inji sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane.
Tun bayan da Gwamnatin Najeriya ta ayyana cewa sojojin kasar zasu aukawa ‘yan ta’addan dajin a cikin watan Janairun da ya gabata wadan nan ‘yan bindiga suka kara zafafa hare-haren su a sassa daban-daban a jihar Nejan al’amarin da ke kara jefa al’umma cikin wani yanayi na tashin hankali da kuma gudun hijira domin neman tsira da rayukkansu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: