Mutanen dai da suka hada mata da yara kanana da kuma maza masu yawan shekaru sun ce sun bar garuruwansu ne saboda neman tsira da rayukansu a sakamakon muggan hare-haren da wadan an 'yan bindiga ke kai masu babu kakkautawa.
Hon. Attahiru Adamu, wani kansila ne daga yankin karamar hukumar Muya, ya kuma ce a yanzu Gundumomi 7 na karamar ta Muya, babu kowa a cikin su.
Kungiyoyin matasa a yankin, na ci gaba da taimakawa 'yan gudun hijirar.
Daya daga cikin shugabannin matasan, injiniya Usman Baba ya ce kashi 60 na manoman yankin Shiroron 'yan bindiga sun raba su da muhallansu.
Hukumomi a jihar Nejan dai sun sha bayyana cewa suna iya kokarinsu wajan shawo kan lamarin da kuma taimakawa yan gudun hijirar, inji Malam Habibu Musa, wani jami’in hukumar ba da agaji ta Jihar Nejan, mai kula da sansanin gudun hijirar na garin Gwada.
Wannan dai duk yana zuwa ne bayan da shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ba da umurnin cewa sojojin kasar su aukawa 'yan bindiga da suka addabi jihar Nejan.