A yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 343, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan kasar da su ci gaba da zama a gidajensu domin kare kansu daga kamuwa da cutar coronavirus.
A halin yanzu an samu Karin mutane sha uku da suka kamu da cutar a Legas, 2 a jihar Edo, 2 a jihar Kano, haka zalika 2 daga jihar Ogun, sai kuma mutunm 1 a jihar Ondo.
Kididdigar da cibiyar dake kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta fitar ta nuna cewa jihohi 19 ne suke da masu cutar a halin yanzu a Najeriya.
A jiya Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya, inda ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na tsawaita dokar hana zirga-zirga a jihohin Legas, Ogun da Abuja babban birnin kasar, tare da yin kira ga ‘yan kasar su ci gaba da hakuri.
Wasu daga cikin mazauna birnin Legas sun koka sakamakon karin wa’adin wannan dokar ta hana zirga-zirga.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum