Tun bayan da aka samu masu dauke da cutar Coronavirus a Kano, gwamnatin ta sanya dokar takaita daukar fasinjoji a ababen sufuri.
Da fari dai ta tsaya a kan masu tuka a dai-daita sahu inda aka basu damar daukar fasinja guda daya tak.
Daga baya kuma gwamnatin jihar ta zauna ta sauya wannan doka in da yanzu ta kai ga sauran masu tuka motocin haya.
Wannan lamarin dai ya janyo korafe-korafe da dama daga masu tuka a dai-daita sahun, inda suke cewa hakan ya jefa su cikin hatsari kasancewar yawancin ababen hawan ba nasu bane ba, kuma dole wadanda suke wa aiki zasu bukaci a kawo musu kudadensu.
A cewar gwamnatin dai an dauki wannan matakin ne domin kare al’umma a jihar daga kamuwa da cutar ta Coronavirus.
Ya zuwa yanzu dai mutum 4 ne aka tabbatar cewa sun kamu da cutar a Kano.
Facebook Forum