Wani mutum mai suna Adel Abdel Bary ya amsa laifi a gaban wata kotun Amurka a New York jiya jumma’a cewa, shi ya kitsa da Osama Bin Laden harin da aka kai kan ofisoshin jakdancin Amurka biyu a Kenya da Tanzania a 1998.
Adel Abdel Bari ya amince a gaban alkalin a New York cewa ya hada kai da Osama Bin Laden da wadansu wajen tarwatsa ofisoshin jakdancin a Kenya da Tanzania. Hare haren sun kasha mutane 224.
Dan shekaru 54 da haifuwa dan kasar masar a shekara ta 2012 Ingila ta tusa keyarsa zuwa Amurka. Galibin rawarda ya taka shine zama masinja tsakanin masu shirya kai harin bam din da kuma kafofin yada labarai. Wadannan sakonnin sun hada da barazanar kungiyar al-Qaida zata kai wasu Karin hare hare.
Dansa Abdel-Majeed Abdel Bary wanda mawaki na zamani a Ingila, yana cikin wadanda ake zargi amma ba’a tabbatar ba da kisan dan jarida ba Amurken nan James Foley. Ana zargin dan nasa ya bar ingila bara ya shiga kungiyar ISIS mai cibiya a Syria.