Cutar Ebola ta kashe wata likita ta hudu a kasar Saliyo cikin likitocin da suka bada karfi sosai wajen yaki da cutar.
Dr. Olivetter Buck shugabar asibitin Lumley dake birnin Freetown ta rasu ne jiya Lahadi kwanaki biyar kacal bayanda aka same ta dauke da kwayar cutar.Jikinta ya yi tsanani ainun yadda ba a iya daukarta zuwa kasar Jamus domin yi mata jinya ba.
Babban jami’in aikin jinya na kasar Saliyo Brima Kargbo ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa, ma’aikatar lafiyar tayi matukar bakincikin sake rasa daya daga cikin wadanda suka bada kai kwarai wajen yaki da cutar Ebola.
A makwabciya Liberia, shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kori manyan jami’an jinya goma bayanda suka yi biris da umarnin da aka basu na komawa kasar domin su taimaka wajen yakar barkewar cutar Ebola,
Wata sanarwar gwamnati tace jami’an guda goma sun nuna halin ko in kula da bala’in da kasar ke ciki.
Kasashen Liberia da Saliyo da kuma Guinea ne barkewar cutar Ebolan tafi shafa, wadda kashe sama da mutane dubu biyu da dari biyar