Karo na biyu ke nan da ma’aikatan makamashi da Ofishin man Petur din Nijer ke zanga-zanga tare da yin zaman dirshan a gaban Ofishin ministan dangane da wani abu da suka kira rashin kulawa da wasu koke-koke da suka gabatar ga Ofishin, wanda yana daya daga cikin ministoci masu muhimmanci a janhuriyar Nijer.
A sanyin safiyar yau, daukacin ma’aikatan sun rurrufe Ofisoshinsu tare da yin kiran taron manema labarai don bayyana masu dalilan da yasa suka tsunduma cikin yajin aiki.
Tsawon kwanaki biyu ne zasu kwashe suna wannan yajin aikin a gaban Ofishin da ma daukacin ofisoshin dake fadin kasar Nijer. A ta bakin mallam Mohammadu Buda, a wata hira da wakilin murya Amurka Abdoulaye Mamane Amadou yayi da shi, Yace yajin aiki zai yi tasiri kwarai, don kuwa zai dagula abubuwa da yawa a kasar.
A nasa bangaren kuma, babban magatakardar Ofishin ministan makamashi Mallam Hassan Garba ya tabbatar ma ‘yan jarida cewa, ma’aikatan sun yi hanzarin tsunduma cikin yajin aiki ne alhali suna ta kokarin warware matsalolin da ma’aikatan ke fuskanta. Mallam Hassan ya cigaba da cewa nan da ‘yan kwanaki za a sasanta.
Kawo yanzu dai ba wani sulhu da aka cimma akan yajin aikin wanda gobe ne rana ta biyu da faraway, ranar da kuma za a kawo karshen yajin aikin.
Kamar yadda za kuji a nan Abdoulaye Mamane Amadou ne ya bada rahoton.