Wani Malam Abdulrahaman Maihula ya kwashe fiye da shekara talatin yana sauraron Muryar Amurka Sashen Hausa. Ya fada haka ne yayin da yake ganawa da tawagar Shugaban Sashen Hausa Mr. Leo Keyen wadda yanzu tana ziyarar aiki a Jamhuriyar Niger.
Malam Maihula yace Muryar Amurka ta zama masu uwa amma an tauye masu hakinsudomin ba kullum ake yada labarin kasar ba a sashen. Domin magance irin wadannan korafe korafen ya sa tashar tana shirin fadada aikinta a kasar kamar yadda shugaban sashen Mr Leo Keyen ya bayyana.
Mr. Leo Keyen yace zasu dauki masu ruwaito rahotanni daga duk yankunan kasar tare da kafa makarantar horas da 'yan kasar yadda ake aikin jarida.
Tawagar Leo Keyen tana cigaba da ziyarta tare da ganawa da mahukuntar kasar Niger.
Ga karin bayani.