Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta yi kakkausan suka ga Larabawa da kasashen Musulmi, kan kumfar bakin da suke yi dangane da halin da Falasdinawa ke ciki, ba tare da sun dauki kwararan matakan magance matsalolin rayuwa da Falasdinawan suke ciki ba, da kuma dafawa shirin zaman lafiyan da ake kokarin tabbatarwa a yankin.
A jiya Talata, Haley ta bayyana hakan a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar, tana mai cewa “magana ba ta da wuyar yi.”
Haley ta kuma ambato kawayen Amurka irinsu Kuwaiti da Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ta ce, ba sa tabuka komai wajen tallafawa hukumar da ke taimakawa ‘yan gudun Hijra ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNRWA a takaice, wacce ke tallafawa Falasadinawa ‘yan gudun Hijra.
“A shekarar da ta gabata, Iran ba ta bai wa hukumar ko kwabo ba, haka ma Algeria da Tunusia, inji Jakadiya Haley.
Sai dai ta ce “akwai kasashen da suka dan tabuka wani abu da suka hada da Pakistan da Masar da suka ba da dalar Amurka dubu 20-20, sai kuma Oman da ta ba da dala dubu 668.
Har ila yau, Jakadiya Haley, ta yi ambaci China wacce ta ba da dala dubu 350 da kuma Rasha wacce ta ba da dala Miliyan biyu duk a bara.
Ta kuma kara da cewa “a bara, yayin da Algeria ta gaza ba da ko sisi, Turkiya kuma ta ba da dala miliyan 6.7, Amurka dala miliyan 364 ta bayar.
Sai dai Haley, ba ta ambaci cewa a watan Janairu, gwamnatin Trump ta zaftare adadin kudin da take bayarwa ba, da dala miliyan 300, lamarin da ya bar hukumar ta kula da ‘yan gudun Hijra, shiga cikin matsalar karancin kudin da ba ta taba fuskanta ba.
A halin da ake ciki kuma, rundunar sojin Isra’ila ta ce ta harbo wani jirgin yakin Syria a jiya Talata, bayan da ya shiga sararin samaniyarta.
Facebook Forum