Makasudin Taron na hadakar shugabannin kwamitocin tsaro na majalisun wakilai na Afirka, wanda ya tattaro ‘yan majalisun nahiyar da ma wakilai daga tarayyar Turai ta EU, da takwararta ta Afirka wato AU, shine yin muhawara akan kalubalen tsaro da ke ciwa nahiyar tuwo a kwarya.
Shugaba Buhari, wanda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilta, ya ce matsalar bullar kalubalen tsaro a kasa daya ka iya shafar makwabtanta da ma shiyyar da kasar ke ciki ko ya ma wuce nan, abinda ya sa daukar matakai na tunkarar al'amarin da ake yi yanzu zama da muhimmanci.
Mr. Roland Stain, na gidauniyyar Konad Adreneur da ya taimaka wajen shirya taron, ya koka kan yadda matsalolin tsaro a Afirka ke kara muni a nahiyar cikin ‘yan shekarun nan duk da irin hobbasan da Afirka da Turai ke yi, yanzu ya zama dole a canza salo a cewarsa.
Shugaban gamayyar jagororin kwamitocin tsaro na majalisun kasashen Afirka, Honarable Sha'aban Ibrahim Sharada, ya ce taken taron shine ''samar da hadin kai tsakanin Turai da Afirka da sabbin dabaru na taimakekeniya,” hakan zai taimaka wajen samar da tsarin tunkarar matsalar da fahimtar da majalisun Turai kan halin da kasashen Afirka ke ciki game da batun tsaro, da kuma muhimmancin shigowa Afirka da taimaka mata wajen yakar ta'addanci.
Honarable Sha'aban Sharada, wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan Najeriya, ya ce haduwar ‘yan majalisun Afirka da na Turai zai taimaka gaya wajen fahimtar da gwamnatocinsu akan abinda ake bukata a Afirka ta bangaren taimaka wa nahiyar domin samar da zaman lafiya.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina.