Samun kudin Dala ga masu tafiya don gudanar da kasuwanci, neman lafiya ko ilimi daga bankunan Najeriya abu ne mai cike da sharudodi da suka hada da ba da wasu takardun shedar bukatar hakan, wanda a wasu lokutan dole masu bukatar gaggawa su je su nema a kasuwar ‘yan canji.
Masana harkar tattalin arziki irin su Kasim Kurfi, na danganta tashin farashin kayayyaki a kasuwanin kasar da faduwar kudin Naira sakamakon yadda ake shigowa da yawancin kayayyaki daga kasashen waje.
Bayan haka ‘yan Najeriya da yawa ba sa ajiye kudinsu a Naira sai Dala a cewarsa.
Shi ma masanin tattalin arzikin kasa Dakta Isa Abdullahi, ya alakanta tashin Dalar da yadda ‘yan Najeriya ke nuna bajintar sayan kayan waje akan na cikin gida.
A cewar Abdullahi, tsarin yanayin tattalin arzikin Najeriya ya ta’allaka ne kan kasashen waje, kuma duk kasar da ba za ta iya samar da abubuwan da ake bukata a cikin gida ba to lallai za a fuskanci matsala.
‘Yan kasuwa, musamman masu kawo kaya daga kasashen waje na ci gaba da kokawa game da tashin farashin Dala, lamarin da ke tasiri sosai ga kasuwancinsu na yau da kullum.
A baya dai babban bankin Najeriya ya ce zai hukunta duk wanda aka samu da laifin amfani da takardun bogi wajen samun kudin dala, bayan samun labarin wasu mutane da ke amfani da wannan damar don samun riba.
A halin yanzu, farashin Dala a kasuwanin bayan fage ya kai Naira 570 a kan ko wacce Dala, abin da ya haifar da gibi akan yadda bankuna ke badawa kan Naira 415.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.