Majiyoyi daga jihar sun bayyana cewa lamarin dai ya auku ne kwanaki kadan bayan da aka biya kudin fansa don kubutar da wani dan kasuwa mazaunin birnin Jalingo da kuma wata matar aure da aka sace 'yan makonnin da suka gabata.
Wata majiya ta bayyana cewa fadan ya afku ne a kusa da wani tsauni da ke karamar hukumar Ardo Kola a jihar ta Taraba in ji jaridar Daily Trust.
Kazalika, wasu mazauna kauyen da ke kusa da tsaunin dutsen sun bayyana cewa sun ji muryoyin da ke fitowa daga wajen dutsen, wanda masu garkuwa da mutanen ke iko da shi suna hayaniya tsakanin juna kafin aka gano gawarwakin mutane 3 din a kusa da wajen.
Rahotanni sun yi nuni da cewa masu garkuwa da mutanen sun gwabza fada a junansu ne lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasunsu.
A cewar mazaunan kusa da tsaunin, wannan shi ne karon farko da aka ga gawarwaki mutanen da ake zargin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne.
Haka kuma, wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwa da mutanen na amfani da hanyar Kogin Mallam Garba da ke birnin Jalingo a matsayin hanyarsu ta zuwa maboyarsu dake tsaunin Kwando.
Majiyar ta kara da cewa a baya an gargadi mazauna kauyukan da ke kusa da yankin da su guji bayyana wa jami’an tsaro ayyukansu a yankin.
Rahotanni daga yankin sun kuma bayyana cewa masu garkuwa da mutanen suna gudanar da ayyukansu cikin walwala a yankin, kuma kusan kullum suna zuwa kan babura, a wasu lokutan ana kawo musu kudin fansa a dajin da ke kewaye, galibi cikin dare.
Duk kokarin ji ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba kan wannan lamarin a yayin hada wannan labari ya ci tura.