A cewar shugaban Cibiyar Horar da ‘yan majalisu a Africa, Dr Usman Danlami Muhammad, mutanen na bukatar taimako domin yawancinsu idan sun fito ba su da madogara.
“Wasansu da yawa muna jin labarin cewa suna neman ‘yan uwansu ne ko iyayensu ko mazajensu ko matansu, wasu an kashe su wasu kuma suna cikin gari sun bazama.” In ji Dr. Muhammad.
Ya kara da cewa yaki wani abu ne da ya kunshi bayan mutum ya tsira yana kuma bukatar wani tallafi na musamman domin ya dawo cikin hayyacinsa.
“Bai kamata ba a ce da an kama su a sake su, ya kamata a zauna da su a tantance su a duba hankalinsu da natsuwarsu, saboda halin ni ‘yasu da suka shiga, wasu sun ga jini wasu sun ga yadda aka kashe ‘yan uwansu.” Ya kara da cewa.
Rikicin Boko Haram a Najeriya wanda ya faro tun daga 2009, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 12,000 kana ya raba wasu miliyoyi da gidajensu, musamman ma a arewa maso gabashin kasar.
Domin jin karin bayani saurari cikakkiyar hirar Dr. Usman Danlami Muhammad da Grace Alheri Abdu: