Kungiyar mayakan nan ta Somaliya mai suna al-Shabab, ta dau alhakin kai wani mummunan hari a wani otel a birnin Mogadishu a yau dinnan Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 11, ciki har da mai otel din, da wani kwamandan soji da wasu 'yan majalisar dokoki biyu da wani dan jarida.
Ministan Tsaron Somaliya Abdirizak Omar Mohammed ya gaya ma Muryar Amurka cewa wasu maharan kungiyar al-Shabab 6 tafe da motoci biyu shake da bama-bamai ne su ka kai hari otel din Sahafi a babbab birnin na kasar Somaliya. Ya ce jami'an tsaro sun kashe dukkannin maharan.
Hukumomi sun ce maharan sun tayar da bama-baman cikin motocin da safiyar yau a mashigar otel din, sannan sai wasu 'yan bindiga su ka abka cikin otel din, wanda jami'an gwamnati da manyan 'yan kasuwa ke fai shiga. Shaidu sun yi ta jin musayar wuta mai tsanani a cikin otel din.
Babban jami'in dan sanda Isma'il Nur ya gaya ma kafar yada labarai ta Reuters cewa 'yan sanda ceto wasu jami'an gwamnati da dama, ta wajen amfani da tsani ta bayan otel din. Ya ce 'yan sanda sun samu kiraye-kiraye daga wasu ma'aikatan otel din da ke boye tare da wadanda su ka ji raunuka.
Daga bisani dai dakarun tabbatar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka da na Somaliya sun shawo kan al'amura a otel din.