Sai kuma gashi a karkashin mulkin shugaba Buhari an soma rade radin cewa kasar na daukan sojojin haya a yakinta da kungiyar Boko Haram.
Dr. Emmanuel Shehu na kungiyar Bring Back Our Girls dake fafutikar ganin an kubutar da 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace ya nuna rashin amincewarsu da yin anfani da sojojin haya.
Yace lokacin shugaba Jonathan da aka kawo sojojin haya daga Afirka ta Kudu yace yin hakan ba daidai ba ne domin duk inda aka kai sojojin haya yana karyawa sojojin kasa gwuiwa. Babu tabbas cewa sojojin hayan ba 'yan leken asirin kasa ba ne. Yanzu da suka soma jin rade radin yin anfani da sojojin haya basu amince da hakan ba.
Muryar Amurka ta tambayi kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Kanar Rabe Abubakar ya kuma musanta zargin. Yace tun lokacin da aka samu sabbin shgabannin sojoji babu wani sojan haya daya cikin sojojin kasar. Ta bakin kakakin wadanda suke da hannu a lamarin can baya su ne suke yada jita-jitar saboda an hanasu yin abun da suke yi da.
Rahotanni sun ambato kakakin hedkwatar tsaron Afirka ta Kudu yana cewa kasarsa bata da dakaru a Najeriya amma ya ki ya ce ko akwai sojojin haya ko babu.
Ga karin bayani.