Gwamnatin jihar Nasarawa, ta karyata rahotanin dake cewa an sami bullar cutar Ebola, a jihar ta Nasarawa.
Kwamishina lafiya, a jihar Nasarawa, Dr. Emmanuel Akabe, yace cutar da aka sami bular ta a wani yanki na jihar it ace cutar kwalara.
Dr. Akabe, ya furta haka ne a hiran da suka yi da wakiliyar mu Zainab Babaji, inda yace “bamu da cutar Ebola a Nasarawa, abun da muka samu satin da ya wuce a Takalafiya shine cutar` kwalara, wadanda kuma suka kamu an yi masu magani kuma sun warke suna gidajen su”.
Ya kuma kara da cewar gwamnatin jihar na daukan matakan kariya domin cutar ta Ebola, da kuma fadakar da kawunan jama’a dangane da matakan dauka inda cutar ta bulla.