WASHINGTON D C —
Shugaban Amurka Donald Trump ya kare kudurinsa na korar shugaban hukumar binciken manyan laiffukka ta FBI, James Comey, inda ya bada hujjar cewa “yanzu, tsakanin ‘yan jam’iyyun Republicans da Democrats, ba daya da ke da amincin cewa Comey na iya gudanar da wannan aikin nashi.”
A cikin sakkonin twitter da dama da ya aika yau da safe, Trump yace za’a sami wani sabon mutum da zai iya jagorancin wannan hukumar ta FBI, “wanda zai maido da kimarta da aka sani.”
Sai dai kuma masu sukar lamirin koran shugaban na FBI daga aikinsa sun ce korar tashi zata saka ayar tambaya gameda binciken da Hukumar ta FBI ke gudanarwa akan katsalandan Rasha a cikin zaben shugaban kasa na Amurka da aka yi a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, inda ake zargin akwai wata cudanaya da ta gudana tsakanin kwamitin zaben Trump da su mutanen na Rasha.
Facebook Forum