Bayan wata ganawar da suka yi a birnin Rome tare da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry. Inda Netanyahun yace, yana ganin wannan wani muhimmin mataki ne don inganta alakar da ke tsakaninsu.
An dai sami baraka a abotar kasashen biyu ne a shekarar 2010, sakamakon ruwan wuta akan jirgin ruwan kayan agaji na Turkiyya, a lokacin da Gaza ba shiga ba fita, sakamakonta na mazaunin shugabancin kungiyar Hamas masu tada kayar baya.
Wani babban jami’in Isra’ila yace, kafin cimma wannan daidaiton alakar, sai da Isra’ila ta nemi afuwar mamayar da ta yiwa jirgin na Turkiyya.
Sannan suka yarda za su biya Turkiyya diyyar Dalar Amurka Miliyan 20 ga iyalan mamata da masu rauni sakamakon harin na jirgin ruwan da aka kai.