Jam’iyyar ta PP ta lashe kujeru 137 akan 14 daga zaben da ya gabata. Sai dai har yanzu suna bukatar karin kujeru kafin su kai ga adadin guda 176 da ake bukata don zama masu rinjaye a cikin majalisar mai wakilai 350.
Kasar Spain din ta sake maimaita zaben na ‘yan majalisar ne bayan da aka kasa cimma matsaya a sakamakon zaben baya da aka yi na watan Disambar bara, wannan aka shafe watannin shida ana neman daidaiton da ya kasa kaiwa ga gaci.
Jam’iyyar masu sassaucin ra’ayi ce ta zo ta biyu a zaben da aka yin a jiyan, tare da lashe kujerun majalisar guda 85. Sai dai a yayin da shi Firaministan ke ikirarin dorewar mulkin jam’iyyarsu, shi kansa har yanzu yana nan a matsayin inda yake a zaben bai matsa ko ina ba.