Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Ministan ‘Yan Gudun Hijirar Afghanistan


Ministan ‘Yan Gudun Hijirar Afghanistan, Khalili ur-Rahman
Ministan ‘Yan Gudun Hijirar Afghanistan, Khalili ur-Rahman

Khalili ur-Rahman, wanda ke cikin jerin sunayen mutanen da Amurka ta sanyawa takunkumi kuma baya bayyana ba tare da bindiga mai sarrafa kanta a hannunsa ba, dan uwa ne ga Jalaluddin Haqqani, wanda ya assasa kungiyar nan ta “Haqqani” da ake matukar tsoro.

Wani harin kunar bakin wake a harabar ma’aikatarsa ta hallaka ministan ‘yan gudun hijirar Afghanistan a yau Laraba, kamar yadda wata majiyar gwamnatin ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na afp.

“An yi rashin sa’a wata fashewa ta afku a ma’aikatar kula da ‘yan gudun hijira kuma minista Khalil ur-Rahman Haqqani da wasu abokan aikinsa sunrasa rayukansu,” a cewar wani jami’in da ya nemi a sakaya sunansa.

Ya kara da cewar harin kunar bakin wake ne ya haddasa fashewar.

Khalili ur-Rahman, wanda ke cikin jerin sunayen mutanen da Amurka ta sanyawa takunkumi kuma baya bayyana ba tare da bindiga mai sarrafa kanta a hannunsa ba, dan uwa ne ga Jalaluddin Haqqani, wanda ya assasa kungiyar nan ta “Haqqani” da ake matukar tsoro wacce ke da alhakin kai munanan hare-hare yayin shekaru 20 din da kungiyar Taliban ta shafe ta na tada kayar baya.

An ce ‘ya’yan zuri’ar ta Haqqanin sun shiga kokuwar neman iko a tsakanin hukumomin Taliban

A cewar rahotannin kafafen yada labarai, sun yi zurfi wajen nuna adawa da magoya bayan tsagin dake da tsauri wajen bin shari’ar Musulunci a bisa fahimtar babban jagoran kungiyar Taliban dake zaune a Kandahar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG