Umurnin, wanda ake kira, "Umurnin Sayen Na Amurka, Daukar Dan Amurka Aiki," zai fara aiki ne bayan wani tanajin da ke tafe da shi ya kwaskware tsarin takardar visa ta H 1-B.
Takardar visar ta H1-Bs ta amince ma kamfanoni - musamman ma na fasahar lataroni - su dau kwararru daga kasashen wace su yi aiki a AMurka na tsawon shekaru uku. Kowace shekara akan ware gurabe 85,000 na daukar irin wadannan ma'aikatan, inda gurabe 65,000 na masu digirin farko ne a yayin kuma 20,000 na masu digiri na biyu ko fiye.
"Za mu yi amfani da abin da dukkanninku ku ka sani sosai. Ana kiransa gudumu," a cewar Trump a yayin wani jawabi a kamfanin Snap-on Tools da ke Kenosha, Wisconsin a jiya Talata.
Gwamnati za ta dau matakin ganin cewa kamfanin na nuna shaidar cewa irin wadannan visa ana bai wa ma'aikatan da su ka yi matukar kwarewa ne a bangarensu.
Facebook Forum