A wani yanayi da ake mai kallon abu mafi muhimmanci da gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi cikin watanni 17 da ta kwashe tana mulki, Trump ya sauya wani tsari, ya kuma ba da umurni na gashin-kansa, wanda ba sai ya nemi iznin majalisar dokoki ba, inda ya soke dokar nan da ta ba da damar a raba yaran bakin haure da iyayensu da suka shiga Amurka ta kan iyakar kudancin kasar da Mexico, ba bisa kai’da ba.
Yayin da yake rattaba hannun akan wannan sabon umurni, gabanin ya kama hanyarsa ta zuwa wani gangamin siyasa a jihar Minessota a jiya Laraba, shugaba Trump ya ce “wannan mataki ne na kokarin barin iyalai a tare, da kuma kokarin ganin an samu kan iyaka mai cikakken tsaro.”
Sauya wannan tsari da Trump ya yi, ya biyo bayan suka da jami’an Republican da na Democrat suka yi ta yi, wadandan suka hada kai suka kira lamarin na raba yara da iyayensu, a matsayin “rashin imani.”
Matakin karbe yaran, ya bar iyaye cikin duhu kan inda ‘ya’yansu suke ko kuma ta yaya za a sake hadasu.
Wannan umurni zai fara aiki ne nan take bayan rattaba hannun da shugaban ya yi, a cewar Gene Hamilton, mai bai wa babban Attonery Janar din Amurka, Jeff Sessions shawara, amma ya ce, akwai matakan da za a bi wajen aiwatar da wannan umurni.
Facebook Forum