Jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ba zata zama sansanin bakin haure ba, kuma ba zata zama inda za’a ajiye ‘yan gudun hijira ba. Shugaban yayi wannan furucin ne a fadar sa ta White House a yayinda ake ta nuna bacin rai dangane da matakin da gwamnatin sa ta dauka na raba yara da iyayensu akan iyakar Amurka da kasar Mexico.
Wannan mataki yasa matan tsoffin shugabanin Amurka guda uku suka yi Allah wadai da wannan manufa ta shugaba Trump na raba yara da iyayensu wadanda suka shiga Amurka ta barauniyar hanya. A ranar Lahadi ne jaridar Washington Post ta buga labarin cewa matar tsohon shugaban Amurka George Bush, Laura ta baiyana manufar a zaman na rashin tausayi da bai dace ba.
Haka ita ma Michele, matar tsohon shugaba Barack Obama ta maida martani akan wannan mataki ko manufa.
Ita ma matar tsohon shugaban Amurka, yar takarar shugabar kasa ta jam’iyar Democrat Hillary Clinton ta fada a jiya Litinin cewa al’amarin akan iyakar Amurka da Mexixo dake kudancin kasar rikicin jin kai ne, kuma abinda ke faruwa ga iyali can yana da ban tsoro.
Kai hatta matar shugaba Trump Melania, ita ma bata goyi bayan wannan manufar ta mijin ta ba. Ta gabatar da sanarwar da ba saban saboda da wuya ta yi magana amma a ranar Lahadi akan wannan batun ta mayar da martani. Melania Trump tace ta tsani ta ga an raba yara da iyayensu.
Facebook Forum