Wannan matakin kuma ya fusata su da gwamnatin shugaba Donald Trump da matakan da take dauka akan bakin hauren dake shigowa a kasar bada izni ba, a cikin halin da ta kira na “ba sani, ba sabo.”
Wata kafar watsa labarai mai zaman kanta mai suna ProPublica ce ta sako wannan sautin mai tsawon kusan mintoci takwas, wanda kuma tace wani mutume ne mai akidar tone-tonen assirai da ba’a tantace sunansa ba, ya bada shi ga wasu lauyoyi.
Daya daga cikin muryoyin da ta kara fusata mutane itace muryar wata ‘yar karamar yarinyar da ake jin shekarunta na haihuwa ba zasu shige 6 ba, wacce kuma ake jin ‘yar asalin kasar El-Salvador ce, da aka ji tana magana da harshine Latinanci, tana rokon jami’ai da su kira gwaggonta ta zo ta dauke ta daga gidan wakafin da ake tara yaran da ake kwacewa daga iyayensu.
Shugaba Trump dai ya kare hujjar daukan wannan matakin na raba yaran da iyayensu akan iyakar Amurka da Mexico da cewa Amurka ba zata zama wata mafakar ‘yan gudun hijira ba.
Facebook Forum