Sanarwar ta caccaki gidan talabijin din da ya bada rahoton cewa kudin harajin da shugaban ya biya ya sabawa doka.
Sanarwar, wadda ta fito da yammacin jiya talata, an bada ita ne jim kadan kafin wani rahoton da gidan talabijin na MNSBC, ya bayyana a cikin shirin Rachel Maddow wanda ta bada wannan bayanin dake kunshe cikin shafi biyu na harajin Trump na shekarar 2005.
Ta ce wani mai sharhi akan harkokin haraji ne ya bada wannan bayanin.
Johnston ya shaidawa Maddow cewa yasamu wadannan bayanan ne cikin akwatin karban sakonninsa na gidan waya, kuma bai san ko wanene ya aiko masa da shi ba.
Maddow tace wannan yasa ta aike da wadannan takardun zuwa fadar White House domin neman Karin bayani.Ta ce amma sai fadar ta gwamnati ta shiga tallata wannan bayanin tun ma kafin ta fara gabatar da nata shirin a cikin daren jiya talata.
Facebook Forum