Daga nesa ana hangen hayaki a yau lahadi daga sararin samaniyar birnin a yayin da ake jin karar fashewar nakiyoyi.
Tun daga lokacin da gwamnati ta fara kutsawa cikin yammacin birnin a farkon 19 ga watan Fabrairu, Kwamandojin Amurka da na Iraqi sun bayyana irin tsananin jajircewar da dakarun 'yan tsagerun sukayi wajen jan tunga a biranen da suke da matukar amfani a kasar da yaki ya tarwatsa.
Dakarun gamayyar da Amurka ke jagoranta , wadanda aka kai musamman domin horaswa da kuma bada shawarwari, sun taimaka wa dakarun Iraqi wajen yakin na Mosul.
Dakarun na Iraqi sun sake kwace bangaren gabashin birnin a wannan shekarar bayan kazamin harin da suka kai a watan Oktobar bara.
Major Janar Maan Al-Saadi na dakarun Iraqi ya fadawa kafar yada labarai ta Faransa cewa “Kusan kaso uku “ na yammacin Mosul na karkashin Ikon Dakarun Iraqi ne.
Facebook Forum