Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Je Biranen Dayton, El Paso Domin Yin Ta'aziyya


Shugaban Donald Trump ya kai ziyara tare da mai dakinsa, don jinjinawa wadanda suka fara kai daukin farko da kuma tattunawa tare da iyalai da suke zaman makoki da wadanda suka tsira daga wannan bala’in.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya isa Dayton, daya daga cikin biranen da aka kai hare-haren bindiga a karshen makon da ya gabata.

A yau Laraba shugaba Trump, zai kai wata ziyarar garin El Paso na jihar Texas da yake kan iyaka ta kudu maso yammacin kasar, wanda shi ma a karshen makon da ya gabata aka kashe mutum sama da 20.

Mazauna birnin na El Paso sun daura alhakin faruwar wannan lamari akan shugaban kasar saboda irin kalamansa da yake yi, wadanda ke ta da hankali, inda suka bukace shi da kada ya zo.

Jami’an fadar White House sun ce ziyarar ta shugaba Trump da zai kai irin wacce ya saba kai wa a duk lokacin da aka samu irin wannan hari na kan mai uwa da wabi.

A baya, shugaban na Amurka ya kai ziyara Parkland da ke jihar Florida da Las Vegas na jihar Nevada, wadanda duk garuruwa ne da aka kai hare-hare.

Fadar ta White House ta ce, zai kai ziyarar tare da mai dakinsa don jinjinawa wadanda suka fara kai daukin farko da kuma tattunawa tare da iyalai da suke zaman makoki da kuma wadanda suka tsira daga wannan bala’in.

Mai magana da yawun fadar White House, Hogan Gidley, ya fada jiya Talata cewa, Trump yana so ya je wadannan yankuna da suke cikin alhini, domin su yi addu’o’i tare, ya kuma yi musu ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG