Shugaban Amurka Donald ya ce da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ba abokinsa ba ne sannan kuma ba abokin adawarsa ba ne da kwanaki kalilan gabanin haduwar shugabannin biyu a wani taron kolin da aka shirya.
A lokacin ganawarsa da manema labarai yau a wajen taron NATO da ake a Brussels, Trump yace Putin “Ba makiyina ba ne. Abokina ne? A’a, ba wani dogon sani na yi mishi ba, amma a ‘yan lokuttan da muka hadu, mun mutunta juna sosai.”
Sai dai duk da haka, Trump ya bayyana Putin da cewa “shi mutum ne haziki, mai kuzari, wanda watakila wata rana zai iya zama abokina.”
A ranar Litinin mai zuwa ne aka shirya za’ayi taron koli tsakanin shugabannin na Amurka da Rasha a Helsinki, inda Trump yayi alkawarin cewa zai tado maganar Yarjejeniyar Rage Miyagun Makamai, da yadda Rasha ke sabawa Yarjejeniyar da aka kulla kan batun Rundononin Sojan Nukiya da kuma katsalandan din da ake zargin Rasha da yi a cikin zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016.
Facebook Forum