Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Gargadi Iran Akan Matakin Da Ta Yi Barazanar Dauka


Mike Pompeo yayinda ya isa Brussels inda ya gargadi Iran
Mike Pompeo yayinda ya isa Brussels inda ya gargadi Iran

Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amurka ya ce Iran zata dandana kudarta idan ta aiwatar da barazanar katse hanyoyin shigar da mai a yankin Gabas ta Tsakiya

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, na ci gaba da nuna matsin lamba ga Iran tare da yi mata gargadin cewa, “za ta dandana kudarta” bayan da hukumomin Tehran suka yi barazanar katse hanyoyin shigar da mai a yankin Gabas ta Tsakiya.

A jiya Talata, Pompeo ya isa Brussels, inda ya tsara zai yi wasu jerin taruka a gefen taron kungiyar tsaro ta NATO, domin ya tabbatarwa kawayen Amurka cewa Iran ba za ta yi nasara ba.

Gabanin zuwansa Brussels a jiyan, Pompeo ya kai wata takaitacciyar ziyarar a Hadaddiyar Daular Laraba, inda ya ce “Amurka ta himmatu wajen tabbatarwa shugabannin Iran cewa irin dabi’un da suke nunawa, ba za su haifar mata da sakamko mai kyau ba.”

A makon da ya ne, shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi barazanar cewa, za su katse hanyar da ake safarar man kasa da kasa da ake bi da shi ta mashigin Hormuz, idan har Amurkan ta ci gaba da yunkurin tilasatawa dukkanin kasashe su daina sayen manta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG