Shugaba Donald Trump, ya isa birnin Brussels, inda a nan ne hedkwatocin kungiyar tsaro ta NATO, da kuma ta Tarayyar Turai suke, wadanda duk bangarori ne biyu da shugaban na Amurka ke ci gaba da yin hannun babbar-riga da su.
A jiya Talata, Trump ya soki kungiyoyin biyu, inda a shafinsa na Twitter ya fito karara, yana kira ga mambobin kungiyar, da su kara kudin karo-karo da suke bayarwa na tsaron kawancen kungiyar, wanda ya kasance mai muhimmanci ga kawancen dakarun kasashen yammaci, tun bayan yakin duniya na biyu.
Cikin watanni 17 da gwamnatin Trump ta kwashe tana mulki, shugabannin nahiyar turai suke ta nuna damuwa da fushi kan yadda Trump yake sukarsu, amma kuma suke taka-tsatsan wajen sukarsa a fili.
Amma kuma hakan ya sauya a jiya Talata, a daidai lokacin da shugaban na Amurka ke shirin yin wannan tafiya zuwa ketaran tekun Atlantika.
A wani martani da shugaban gudanarwar kungiyar ta tarayyar turai Donald Tusk ya mayar, ya ce, “ya ke Amurka! ki rungumi kawayenki hannu bi-biyu, domin wadanda ki ke da su ba su da yawa,” yana mai cewa al’adar “sukan nahiyar turai a kulluyaumin” ba hanya ce mai kyau ta tafiyar da kawaye ba.
Da aka tambayi shugaba Trump kan me zai ce game da kalaman na Tusk, sai ya ce “Amurka na da kawaye da dama, kawai dai ba za mu bari ana kwararmu ba ne, kungiyar tarrayar ta turai ta jima tana kwarar Amurka.”
Facebook Forum