Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Shakkun Sahihancin Zaben Amurka Mai Zuwa


Trump
Trump

Shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da bayyana shakkun a kan ingancin zaben kasar na ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaba Trump ya nuna damuwa kan yiwuwar tafka magudi a zaben ta hanyar aikewa da sakwanni, wani salo da jami’ai da dama suka ce ana yi wa karin gishiri da yawa.

“Muna son tabbatar da zaben ya kasance cikin gaskiya da adalci, amma kuma ina shakkar haka,” Trump ya fadawa manema labarai a ranar Alhamis, a fadar White House jim kadan kafin ya shiga jirgi mai saukar ungulu zuwa North Carolina da Florida.

Trump ya yi ikirarin cewa “an gano wasu takardun kuri’a masu yawa a cikin tafki” kana wasu takardun kuri’a dake dauke da sunan Trump, “an zubar da su a cikin kwandon shara.”

An lalata tare da zubar da wasu kuri’u kalilan inda aka ga 9 daga cikinsu a wani bincike, a cewar ofishin babban lauyan Amurka a gundumar tsakiyar Pennsylvania.

Shugaban kasar dai ya yi ta bayyana damuwar sa a kan shirin da wasu jihohi suke yi kamar California, Colorado, Hawaii, Nevada, New Jersey, Oregon, Utah, Vermont and Washington, na aikewa kai tsaye da takardun zabe ta gidan waya zuwa ga mazauna jihohin su yi amfani dasu su yi zabe.

A ranar Alhamis ‘yan majalisar dokokin Amurka suka dauki wani mataki na amincewa da matsaya daya ta tabbatar da kudurin majalisar na ganin mika mulki ga sabuwar gwamnati, kamar yadda kundin tsarin mulkin Amurka ya tanada.

‘Yan jam’iyyar Republican a majalisar suna jaddada muhimmancin hakan ne kwana daya bayan da Trump ya ki amincewa da haka idan dan takarar Democrat Joe Biden ya kayar da shi a zaben, wanda bai fi 40 a gudanar da shi ba.

To sai dai ‘yan jam’iyyar Democrat sun caccaki shugaban kasar akan martanin na sa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG