‘Yar takara karkashin jam’iyyar Democrat Kamala Harris ta ce za ta zake wajen ganin ta samar da kudade ga bankunan al’uma don taimakawa ‘yan Latino wajen kafa wuraren kasuwanci.
A nasa bangaren dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump ya yi ta caccakar abokiyar hamayyarsa a wani taro da aka shirya don al’umar Latino a ranar Talata.
Yayin da take mayar da martani kan ikirarin da Trump ya yi cewa ita mai ra’ayin gurguzu ce, Harris ta ce: “Ni ‘yar jari hujja ce, asalin ‘yar jari hujja.”
Trump ya kuma kwatanta Harris a matsayin “malalaciya” ya kuma yi magana kan matsanancin iko da shugaban kasa ke da shi yayin wasu kalamai da ya yi a wajen shakatawarsa da ke wajen birnin Miami.
Ita dai Harris ta ce za ta mayar da hankali wajen rubanya adadin mutanen da ke aiki wadanda suke da rajista.
Ta kuma jaddada yadda za ta sa a cire bukatar gabatar da shaidar karatun kwaleji don neman aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya inda ta kuma yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su ma su bi wannan layi.
Sannan ta ce za ta samar da damar da za a yafewa masu kananan sana’o’i miliyan daya bashin dala 20,000.
Shi dai Trump na fatan ya shawo kan al’umar Latino wajen nuna musu cewa shi dan kasuwa ne da ya kamata su aminta da shi, duk da cewa yana kiran da a kori bakin hauren da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
Dandalin Mu Tattauna