Trump wanda ke takara karkashin jam’iyyar Republican ya yada zango a wurare uku a ranar Litinin a jihar North Carolina ciki har da inda ya kai ziyara yankin Ashville da guguwa ta yi ta’adi.
Harris a nata bangaren ta maida hankali ne wajen kai ziyara yankunan da ke wajen gari a jihohin da ke tsakiyar yammcin Afirka da ake gwagwagwa a lokacin zabe inda ta hadu da Liz Cheney ta jam’iyyar Republican.
Trump dai ya ci gaba da caccakar Harris a gangamin yakin neman zaben da ya yi a Greenville da ke jihar North Carolina inda ya kwatanta ta a matsayin “mara hankali” sannan ya ce ba ta da tausayi da kwarin zuciya.
Ya kuma soke ta da neman tallafin kudi a San Francisco da ta yi fama da matsalar ibtila’in guguwa.
“Kamala Harris ba ta da tausayi ko basira ko karfin zuciyar da za ta zama Shugabar Amurka. Sam ba za ta iya aikin ba.” In ji Trump.
A nata bangaren Harris ta ce ya kamata a rika daukar kalaman Trump da muhimmanci maimakon a rika kore su ana musu kallon “abin dariya na wanda ba shi da lafiya.”
“Wasu na kallon kalaman nasa a matsayin abin dariya, abin da yake fada shirme ne. Amma ya kamata a fahimci cewa abu ne da ya kamata a sa masa ido sosai.” Harris ta ce.
Harris ta yi nuni da kalaman Janar Mark A. Milley mai ritaya wanda ya rike mukamin shugaban hafsan hafsoshin sojin Amurka a mulkin Trump na farko wanda ya kwatanta Trump a matsayin “tsattsauran mai mulkin kama karya.”
Dandalin Mu Tattauna