Sauya matsayin da Amurka tayi kan matakan da zata dauka kan Korea ta Arewa dake barazana ga yankin Asiya, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pyongyang take ci gaba da gwaje gwaje makamanta masu lizzami da kuma kyautata zaton da ake yi cewa, tana shirin gwada makamin nukiliyarta na karkashin ‘kasa karo na shida.
Da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Bloomberg a jiya Litinin, shugaban yace idan ganawa da shugaban Korea ta Arewar ya dace to zan so in gana dashi. Yace akasarin yan siyasa ba zasu fadi haka ba, yace amma ina fada muku cewar zan so in gana da shi idan akwai yanayin da ya dace.
Ya bayyana haka ne yayin wata hira ta minti 30 da aka yi dashi a ofishinsa na fadar shugaban kasa (Oval Office), a daidai lokacin da dakarun ruwan Amurka suka doshi yankin Koriya .
A wata hira da tashar talabijin ta CBS ta watsa shekaranjiya Lahadi mai take Face the Nation, shugaban ya bayyana sha’awar Kim Jong Un da ya iya samun cikakken iko a kan kasar da ya gada daga mahaifinsa yana dan shekaru ishirin, ya bayyana shi a matsayin mai basira.
Facebook Forum