"Zan kuma gaya ma ka, ba tsammanin Shugaban kasar China, wanda mutum ne da ake mutuntawa, zai yi murna shi ma," abin da Trump ya fada game da Xi Jinping kenan a wata hirar da aka yada jiya Lahadi a shirin "Face the Nation" na gidan talabijin din CBS.
Da aka tambaye shi ko ma'anar ransa "zai bace" da sake gwada makamin nukiliyar Koriya Ta Arewar na nufin idan aka sake zai dau matakin soji kan gwamnatin Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un kenan, sai Trump ya ce, "Ban sani ba, bari dai mu gani. Komai na iya faruwa. Ni kawai dai ba na son a san abin da ke zuciya ta."
Koriya Ta Arewa, wadda ke kokarin kirkiro makami mai linzami mai dogon zango, wanda zai iya dira Amurka daga nisan kilomita 9,000, ta yi wani sabon gwajin na makami mai linzami shekaran jiya Asabar, to amma Koriya Ta Arewa ta ce wannan karon ma gwajin bai yi nasara ba.
A wani sakonsa na twitter, Trump ya ce gwajin ya "saba ma fatan China da Shugabanta da ake matukar girmamawa..." To amma a hirar ta CBS, Trump ya ce sannu a hankali "Koriya Ta Arewa za ta samu tsari mai kyau."
Facebook Forum