Al’ummar garin Ogale dake karamar hukumar Eleme ta jihar Rivers sun gudanar da zanga-zanga a kan matsalar malalar mai da suke zargin reshen kamfanin mai na Shell da haddasawa.
Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye da suka rubuta korafe-korafensu.
A ranar 5 ga watan Fabrairun da muke ciki reshen kamfanin Shell na Najeriya ya ba da rahoton samun malalar mai a Ogale, kusa da birnin Fatakwal, lokacin da wani ramin tattara dagwalo ya yi ambaliya yayin aikin wanke bututu.
Kamfanin ya kara da cewa tawagar karta kwana a kan malalar ta yi martani tare da tsayar da ambaliyar da kuma sanar da hukumomi, inda ya kara da cewa ana tsare-tsare a kan yadda wata tawaga karkashin jagorancin masu sanya idanu za ta nazarci musabbabi da kuma tasirin malalar man.
Dandalin Mu Tattauna