Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa bindigogi 3, 907 sun yi batan dabo daga rumbun adana makaman ‘yan sanda kafin nada Kayode Egbetokun a matsayin babban sufeton ‘yan sandan kasar.
A sanarwar da ya fitar, kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi, yace batagari ne suka yi awon gaba da wasu makaman yayin tarzoma.
Ya kara da cewa, rundunar na so ta yi karin haske a kan cewa akwai alamun rahoton ya samo asali ne daga binciken da ofishin babban mai binciken kudi na tarayya ya gudanar tun a shekarar 2019, wanda mai yiyuwa ya tattara bayanan da suka gabaci wa’adin jagorancin babban sufeton ‘yan sanda mai ci.
“A cikin rahoton, a cewar sashensa na 3b, karamin sashe (iii), an bayyana cewar ba’a san inda bindigogi 3, 907 suka shiga ba amma basu bata ba sabanin yadda ake yadawa a labarai.
Karin hasken na zuwa ne kwanaki bayan da kwamitin Majalisar Dattawa akan asusun ajiyar gwamnati ya bayyana tsananin damuwa game da al’amura da dama dake da nasaba da rundunar ‘yan sandan Najeriya, ciki har da almundahanar kudade da batan makamai.
Dandalin Mu Tattauna