Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar NLC Ta Gudanar Da Zanga-Zanga A Fadin Najeriya Sakamakon Matsalar Tattalin Arziki Da Yunwa


Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar
Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar

Mambobin Kungiyar Kwadago ta Najeriya wato NLC sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar sakamakon matsin rayuwa, yunwa da tabarbarewar tattalin arziki a kasar.

Zangar-zangar na zuwa ne biyo bayan da kungiyar kwadagon da gwamnatin tarayyar kasar suka gana a jiya Litinin, a wani mataki na kawo tsayar da zanga-zangar, amma taron ya kare ba tare da an cimma matsaya ba tsakanin bangarorin biyu.

Tun da misalin karfe 7 na safe ne mambobin kungiyar ta NLC suka fara taruwa a sassa daban-daban na Najeriya, dauke da kawalaye mai dauke da mabambantan sakonni da kuma sanya tufaffi mai tambarin kungiyar NLC.

'Yan Kungiyar Kwadago ta NLC
'Yan Kungiyar Kwadago ta NLC

Sakonnin mabambanta dake kan kwalayen da mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya suka rike sun hada da ''a kawo karshen yunwa da matsin tattalin arziki a kasar'', ''gwamnati ta sake salo wajen sauraron koken al’umma ganin yadda talaka baya iya samun abinci'', "a yau ana sayar da buredi a kan naira 1500".

Zanga-Zangar kungiyar Kwadago ta NLC
Zanga-Zangar kungiyar Kwadago ta NLC

A birnin tarayya Abuja, mambobin kungiyar NLC sun taru a harabar hedikwatar kungiyar dake unguwar Central Area sannan suka fara tattakin zangar-zangar daga nan har zuwa majalisun tarayyar Kasar.

Mambobin kungiyar NLC sun taru a harabar hedikwatar kungiyar dake unguwar Central Area
Mambobin kungiyar NLC sun taru a harabar hedikwatar kungiyar dake unguwar Central Area

A jihar Neja dake makwabtaka da birnin tarayya Abuja, shugaban kungiyar kwadago ta NLC a jihar ne ya jagoranci mambobinta zuwa harabar majalisar dokokin jihar sakamakon halin matsin rayuwa da ‘yan kasa ke ciki da kum yadda mambobin kungiyar ke ci gaba da kokawa kan mummunar tasirin da hare-haren ‘yan bindiga da sauran miyagu ke yi ga matsalar yunwa da ake ciki.

A wani bangare kuma wasu ‘yan Najeriya karkashin kungiyar kare hakkin fararren hula wato Network of Civil Society for Accountability sun fito zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaba Bola Tinubu inda suka rike takarda mai mabambantan sakonni kamar “dole ne mu yi hakuri da Shugaban Kasa mu bashi lokaci don kawo sauyin da ake bukata a kasar.

Magoya Bayan Tinubu
Magoya Bayan Tinubu

Kungiyar NLC dai na zanga-zangar nuna halin matsin da ake ciki a kasar na yini biyu don farkar da gwamnati a kan nauyin da ya rataya a wuyanta.

A saurari rahoton Halima Abdularauf:

Kungiyar NLC Ta Gudanar Da Zanga-Zanga A Fadin Najeriya Sakamakon Matsalar Tattalin Arziki Da Yunwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

A kudau maso yammacin Najeriya, wakilan kungiyar kwadagon sun bi sahun mambobinsu na jihohin Najeriya wajen gudanar da zanga zangar lumana domin nuna adawa da tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.

A jihar Legas, yan kwadagon dai sunyi gangami ne a babbar tashar motoci ta Ikeja dake kusa da shelkwatan rundunan 'yan sandan Legas inda suka rinka rera wakokokin ma'aikatq domin tsumayar dasu.

Zanga Zangar Kungiyar Kwadago jihar Legas
Zanga Zangar Kungiyar Kwadago jihar Legas

A lokacin wannan tattakin dai an ga Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Legas tare da jami'ansa na rakiya ga masu zanga zanga domin tabbatar da doka da oda.

A lokacin zanga zangar dai yan kwadagon dake samun goyon bayan mutanen gari, sun bayyana takaicin yarda gwamnati taki cika alkawarin data sanya hannu da ita a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Yadda Aka Gudanar Da Zanga-Zanga A Legas Sakamakon Matsalar Tattalin Arziki
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00

Yarjejeniyar da aka sa hannu domin tallafawa ma'aikata rage radadin cire tallafin mai.

Rahotanni daga sauran jihohin yammacin Najeriya,irin su Oyo, Ogun, Ondo, Osun da Ekiti na cewar an gudanar da gangamin ba tare da tashin hankali ba, kuma yansanda sun bada kariya ga masu zanga zangar da sauran al'umar gari.

Hakazalika, a jihar Oyo mambobin NLC sun shiga zanga zangar gargadi na kwanaki biyu.

Shugaban Kungiyar a jihar, Kwamred Kayode Martins, ya ce rayuwa ta yi wuya a Najeriya saboda tsadar kayan masarufi.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya shiga zanga zangar inda ya ce masu zanga zangar na da damar nuna rashin jin dadinsu akan halin da kasa ke ciki ya kuma sha alwashin mika wasikarsu ga Shugaba Tinubu.

A saurari rahoton Hassan Tambuwal:

An Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Ibadan Na Jihar Oyo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

A gobe ma za'a ci gaba da gudanr da wannan gangami.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG