Wasu sunyi harbe-harben bindigogi bayan fashewar bama-bamman. Wani gidan saukar baki da yan kasashen waje ke yawan zuwa, nan ne inda ake nufin kai hare haren. Wata rundunar musamman ta Afghanistan ta gaggauta isa wurin inda tayi musayar wuta da wasu yan bindiga biyu da suke kokarin shiga ginin.
Sai dai nan take, babu wani labarin mutuwa kuma bau wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.
Wasu sa’o’I kafi hakan, wani mai harin kunar bakin wake ya tada ban dinsa kusa da ma’iaktar tsaron Afghanistan, a yayin da mutane suka taru suna kallon fashewar da aka fara samu.
Wata tashar telbijin Afghanistan mai suna Tolo TV ta rawaito babban komanda ma’aikatar tsaron General Abdul Raziq tare da shugaban hukumar leke asiri na birnin da shugaban yan sandar lardin suna cikin wadanda suka mutu a harin.
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid yace yace kungiyar tsagerun ce keda alhakin kai wannan harin, suna ikirarin kashe mutane 60, yawancinsu jami’an tsaron Afghanistan ne, koda yake kungiyar ta’addan ta saba Karin adadin mutuwar mutane a irin wa’yannan hare hrae da take kaiwa.