Kwamandan jami'an tsaron farin kaya na kasar Manjo Janar Hamad bn Abdulaziz si ya sanar da hakan yau Litinin.
Yace jami'an tsaron sun shirya tsaf domin bada duk wata kariya ga alhazai a lokacin gudanar da aikin hajji.
Masu nazari akan alamuran tsaro na ganin matakin ya dace.bisa ga la'akari da yadda kasar ke kara fuskantar kalubalen tsaro. Ko a gwanakin baya an samu tashin bamabamai a kasar da suka hallaka jama'a.
A cikin wuraren da aka kaiwa hari har da masallacin Annabi Muhammad (SAW) dake birnin Medina.
Alhaji Musa Suleiman dake kula da harkokin tsaro na kasa da kasa da yake aikin hajjin bana daga Najeriya yace hakika Saudiya tayi rawar gani wajen samo sabbin motocin tsaro. Yana goyon bayan matakan tsaro da kasar ta dauka.
Ga rahoton Nasiru Batsari da karin bayani