Jama'a da sauran wadanda suka halarci taron da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya shirya kan yaki da cutar kwalara sun yaba da wannan taron a zaman wanda ya taimaka wajen dada ilmantar da jama'a da su kansu jami'ai da hukumomi.
"Wannan taro dai abu ne da za a iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu, saboda duk sakonnin da ake son jama'a su ji su fahimta, sun ji din," in ji Umar Abdullahi, jami'in yada labarai na ma'aikatar kiwon lafiya ta Jihar Bauchi. Ya ci gaba da cewa, "abin ya kayatar musamman idan aka yi la'akari da tsarin yin tambayoyi ma jama'a a karshen kowace kasida da kwararru suka gabatar."
Wannan taro dai ya samu halartar mutane masu yawa daga nan Jihar Bauchi da kuma jihohin dake makwabtaka da ita. Kwamishinan kiwon lafiya na Jihar Bauchi, Mohammed Yahaya Jalam, shi ya bude taron a madadin gwamna Isa Yuguda na Jihar Bauchi.